Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kasar Iran ya bayyana cewa kasashen Iran, Pakistan, Turkiyya, Saudiya, Jordan da kuma Indonasia ne suka gabatar da wannan bukatar ta samar da irin wannan rana a gaban MDD, wacce daga karshe majalisar ta amince da bukatar.
Sabon kudurin ya yi allawadai da dukkan magata ta batanci, da cutar da musulmi saboda addininsa, sannan ya bukaci hakuri da juna da kuma zaman lafiya tsakanin musulmi da sauran mabiya addinai daban-daban a duniya.
Banda haka kudurin ya bukaci MDD da kuma sauran kungiyoyin kasa da kasa su raya wannan ranar sannan su wayar da kan mutane dangane da ita a ko wace shekara.
An samar da wannan kudurin ne shekaru biyu bayan da wani harin da wani makiya musulmi da musulunci ya kai hari kan wani masallaci a kasar Sweedziland inda ya kashe musulmi 50 a cikinsa.
A lokacin ne kungiyar OIC ta kasashen Musulmi daga ciki har da kasar Iran suka bukaci a yaki akidar kin musulmi da musulunci a duniya.
342/